Babban Sakataren MDD, Ya Ziyarci 'Yan Rohingyas a Bangaladesh
Jul 02, 2018 11:00 UTC
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres, a'ummar Rohingyas dake gugun hijira a Bangaladesh.
Mista Guteres, ya ce ya kadu matuka, akan bayyanai na kisa da kuma fyade da ya ji daga bakin 'yan gudun hijiran na Rohingyas, dake tsugunne a yankin À Cox's Bazar na Bangaladesh.
A tsakanin watan Agusta zuwa Disamba na bara, sama da 'yan Rohingyas galibi musulmi, 700,000 ne suka tsare daga yankunansu, don kaucewa hahe haren da sojojin Birma ko Myammar ke musu, lamarin da MDD ta danganta a lokacin da yunkurin share wata kabila a doron kasa.
Tags