Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Mayar Wa Trump Da Martani
(last modified Sat, 14 Jul 2018 12:29:26 GMT )
Jul 14, 2018 12:29 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Mayar Wa Trump Da Martani

Ministan harkokin wajen kasar Jamus ya mayar wa Trump da martani dangane da kalaman batunciun da ya yi a kan kasar Jamus.

A zantawar da ya yi da jaridar Der Tagesspiegel ta kasar Jamus, ministan harkokin wajen kasar ta Jamus Heiko Maas ya mayar da martani a kan kalaman da Donald Trump a kan kasar Jamus a taron shugabannin kasashe mambobi a kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels na kasar Belgium.

Ya ce Jamus kasa ce mai 'yancin siyasa, kuma tana yin abin da take ganin maslaha ne ga al'ummar kasarta, saboda haka za ta ci gaba da yin mu'alama da Amurka ne a kan abin yake maslaha ga bangarorin biyu, kuma ba zata amince da cin zarafi da Donald Trump yake yi a kanta ba.

Ya ce a kowane lokaci Trump yana yin maganganu masu jawo tayar da jijiyar wuya a tsakanin mambobin kunyar NATO, inda a zaman Brussels ya kira Jamus da 'yar koren Rasha.