An Fara Tattaunawa Tsakanin Putin Da Trump
(last modified Mon, 16 Jul 2018 18:13:16 GMT )
Jul 16, 2018 18:13 UTC
  • An Fara Tattaunawa Tsakanin Putin Da Trump

A ganawar da Shugabanin kasashen Rasha da Amurka suka fara a birnin Helsinki na kasar Finlande sun tabbatar da aiki tare a fanonni daban daban.

A wannan Litinin ce Shugaban Amirka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suka yi ganawar farko da juya, kafin fara tattauanawar sun shaidawa manema labarai cewa  lokaci ya yi da kasashen biyu za su tattauna kan alakar dake tsakaninsu da ma na duniya.

Putin ya ce Amurka da Rasha kasahe ne masu karfi a Duniya da kashi 90% na makaman nukiliya ke hanunsu, da kuma hakan ba maslaha ba ne ga Duniya dole ne a sake nazari kan wannan batu.

A yayin da yake ishara kan yadda alaka tayi tsami tsakanin  kasashen Amirka da Rasha a shekarun baya-bayan nan, Shugaba Trump na Amurka ya ce Duniya ta sanya  ido a kan tattaunawa ta mu don haka wajibi ne mu kyautata dangantaka a tsakanin kasashenmu.

Shugaban Amurka ya kara da cewa akwai fatan cewa za mu magance matsalolin da suka shafi kasashen biyu kama daga  batutuwan kasuwanci, nukiliya da Siyasa, kuma mu kulla kyakkyawar alaka da babu irinta da kasar ta Rasha.

A gefe guda, kafafen yada labarai sun watsa rahoton cewa saidai shugaba Putin ya jira shugaban Amurka na tsahon awa guda kafin ya iso zauran tattaunawar.