MDD: Musulman Kasar Myanmar Suna Kara Shan Wahala
(last modified Fri, 20 Jul 2018 06:36:39 GMT )
Jul 20, 2018 06:36 UTC
  • MDD: Musulman Kasar Myanmar Suna Kara Shan Wahala

Majiyar Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa har yanzun mutanen kasar Myanmar Musulmi suna ci gaba da shan wahala a hannun gwamnati kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wata tawagar binciken kwakwaob ta majalisar dinkin duniya ce ta bayyana haka a jiya Alhamis bayan wani ziyarar da ta kai sansanin yan gudun hijiran kasar Myanmar a kasar Bangladesh. 

Tawagar ta bayyana cewa a wani tattaunawa da tayi da wadanda basu dade da yin hijra daga yankin Rokhin na kasar ta Myanmar sun tabbatar da cewa har hanzun ana kuntata masu ana kuma hanasu ayyukansu na samun abinci. 

Radhika Coomaraswamy daya daga cikin yan tawagar ta MDD ya ce wani sabon shigowa sansanin yan gudun hijira na Kutupalong a kasar Bangladesh ya shaida masa cewa har yanzun ana hanasu ayyuka kuma babu makaranta ga yayansa don haka ya yanke shawarar yin hijira daga kasar.

A ranar 18 ga wata Satumba na wannan shekara ne ake saran tawagar binciken ta MDD zata gabatar da rahotonta ga hukumar kare hakkin bil'adama mai membobi 47 a birnin Geneva.