Jam'iyyar Imran Khan A Pakisatan Tana Gaba A Zaben Kasar
Sakamakon zaben da aka gudanar a kasar Pakistan ya nuna cewa jam'iyyar tsohon dan wasan criket na kasar Imran Khan ita ce a gaba a dai dai lokacin da sakamakon zaben ya ci gaba da fitowa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Jam'iyyar PTI ta Imran Khan tana gaba a larduna 113 cikin larduna 272 na kasar., bayan an irga kashi 30 na kuri'un zaben a jiya Laraba. sai kuma jam'iyyar Nawaz sharis wanda yake kaso tana gaba a larandun 66 . Biye da su ita ce jam'iyyar tohuwar Priministan kasar Binazir Buto wacce take gaba a larduna 39.
Kafin haka dai hukumar zaben kasar ta Pakistan ta bada sanarwan cewa wasu matsalolin na'ura sun dan jinkirta sakamakon zaben. babar yakoob shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa babu wani magudi da aka yi, sannan da zarar sun warware matsalolin aiko da sakamakon ta na'urotinsu hukumarsa zata bayyana cikekken sakamakon zaben.
sai kuma wani labarin da ke shigowa a yanzu ya ce Imran khan ya lashe zaben kuma zai yi jawabin samun sarana da milisalin karfe huda na yamma.