Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Tana Fama Da Karancin Kudaden Aiki
(last modified Fri, 27 Jul 2018 19:20:02 GMT )
Jul 27, 2018 19:20 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Tana Fama Da Karancin Kudaden Aiki

Babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa majalisar tana fama da karancin kudade.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Antonio Goteres yana fadar haka a wani rahoton da ya fitar, inda ya bukaci ma'aikatar majalisar su rage kashe kudade.

Babban sakataren ya kara da cewa karancin kudaden ya faru ne saboda rashin biyan wasu daga cikin kasashe 193 mambobi a majalisar kasonsu na kudaden da yakamata su biya a cikin lokaci.

Rahoton ya kara da cewan kasasfin kudin majalisar a cikin shekaru biyu shi ne dalar Amurka billon 5 da miliyon 400, wanda aka amince da shi a shekara ta 2017 da ta gabata.

A wani bangaren kuma gwamnatin kasar Amurka ta rage kashe 25% na yawan kudaden da take bawa majalisar saboda sabanin da take samu da wasu matakan da majalisar date dauka wadanda suka ci karo da manufofinta..