Hatsarin Jirgin Sama Ya Hallaka Mutum 18 A Rasha
Hukumomin Kasar Rasha sun sanar da hallakar mutum 18 sanadiyar hatsarin jirgin sama mai saukar angulu a yankin arewa maso yammacin Saiberiya na kasar Rasha.
Jami'ai masu bayar da taimakon gaggawa sun ce jirgin samfurin MI-8 ya yi hatsari ne da misalin karfe 10 da minti 20 agogon yankin (karfe 3:20 agogon GMT) kimanin kilomita 180 daga garin Igarka da ke yankin Krasnoyarsk.
Dukkan wadanda ke cikin jirgin sun mutu - akwai matuka jirgin su uku da fasinjoji 15.
Jirgin na kan hanyarsa ta jigilar ma'aikata masu aiki a wata tashar da ake hako man fetur ne, kuma jami'an 'yan sanda sun fara gudanar da bincike, domin gano musababin hatsarin.
Bayyanan farko sun bayyana cewa matsalar na'ura da kuma kuskuren matukin jirgin ne ya janyo hatsarin.
Kamfanin dillacin labarai na Rasha TASS ya ruwaito cewa tuni aka dauko bakin akwatin jirgin domin gudanar da cikakken bincike akai.