Shugabannin Kasashen Duniya Sun Nuna Damuwarsu Kan "Ta'addancin Nukiliya"
(last modified Sat, 02 Apr 2016 03:50:49 GMT )
Apr 02, 2016 03:50 UTC
  • Shugabannin Kasashen Duniya Sun Nuna Damuwarsu Kan

Shugabannin duniya mahalarta taron duniya akan nukiliya da aka gudanar a birnin Washington na Amurka sun bayyana damuwarsu da yiyuwar amfani da makaman nukiliya wajen ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar shugabannin sun bayyana hakan ne a cikin sanarwar bayan taronsu na kwanaki biyu da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya jagoranta a jiya inda suka ce yiyuwar yaduwar makaman nukiliya da kuma fadawarsu hannun 'yan ta'adda wani lamari ne mai tada da hankali ga duniya da kuma zaman lafiyarta.

Don haka shugabannin suka ce akwai bukatar a yi aiki tukuru wajen ganin an hana cibiyoyin da ba na gwamnati ba mallaka sinadarori masu guba da suke da alaka da nukiliyan don kuwa akwai yiyuwar a yi amfani da su ta hanya mai cutarwa ta bil'adama.

Kafin hakan dai shugaban Amurka Obama ya bayyana cewar akwai jan aiki idan har ana son a hana isar makaman nukiliya zuwa ga hannun 'yan ta'adda irin su kungiyar nan ta Da'esh (ISIS) wanda ya ce a baya ta yi amfani da makamai masu guba kuma tana ci gaba da kokarin makaman makamai masu hatsari.

Daga cikin shugabanni da manyan jami'an gwamnatoci kimanin 60 da suka halarci taron na kwanaki biyu har da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.