Aug 16, 2018 06:43 UTC
  • Mahukuntan Turkiyya Da Jamus Sun Tattauna Batun Harkar Tattalin Arzikin Kasashensu

Waziriyar kasar Jamus da shugaban kasar Turkiyya sun tattauna batun hanyoyin bunkasa harkar tattalin arzikin kasashensu.

A wata zantawa da ta gudana ta hanyar wayar tarho tsakanin waziriyar kasar Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan a jiya Laraba; Shugabannin biyu sun tattauna batun gudanar da zaman tattaunawa kan hanyoyin bunkasa harkar tattalin arziki a tsakanin kasashensu da aka shirya gudanarwa a karshen watan Satumban wannan shekara ta 2018.

Kasar Turkiyya dai tana fuskantar barazanar takunkumin karya tattalin arziki daga kasar Amurka musamman matakin da gwamnatin Amurka ta dauka a halin yanzu na kakaba takunkumi kan ministoci biyu a gwamnatin Turkiyya sakamakon matakin da kasar ta Turkiyya ta dauka na tsare wani malamin addinin Kirista dan kasar Amurka mai suna Andrew Brunson bayan ta zarge shi da hannu a makarkashiyar juyin mulki a Turkiyya a watan Yulin shekara ta 2016.

Tags