Imran Khan Ya Yi Rantsuwar Zama Firayi Ministan Kasar Pakistan
Imran Khan ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon Firayi ministan kasar Pakistan, bayan da jam'iyyarsa ta lashe zaben 'yan majalisar da aka gudanar a cikin watan Yulin da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Imran Khan ya yi rantsuwar ne a fadar shugaban kasar, tare da halartar manyan jami'ai, da kuma wakilan bangarori na al'ummar kasar, gami da manyan hafsoshin sojin kasar da sauran bangarorin tsaro.
Jam'iyar Imran Khan ta samu kujeru 176 daga cikin dukkanin kujeru 272 na majalisar dokokin kasar Pakistan, yayin da jam'iyyar tsohon Firayi ministan kasar da aka tumbuke Nawaz Sharif, ta samu kujeru 96.
Masu adawa da Imran Khan sun yi zargin cewa sojojin kasar sun taimaka masa wajen lashe zaben, zargin da Khan da kuma rundunar sojin kasar suka karyata.