Faransa Ta Amince Da Nasarar Bashar Al-Asad
Ministan harakokin wajen Faransa ya amince da nasarar shugabaBashar Al-Asad na Siriya ya samu a yaki da ta'addanci
A yayin tattaunawar da ya yi da gidan radion kasar, Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya amince da nasarar da shugaba Asad na siriya ya samu a kan 'yan tawaye da kuma 'yan ta'addar da kasashen Duniya ke goyawa baya.
Yayin da yake ishara kan taimakon da kasashen Larabawa da na Yamma ke bawa kungiyoyin 'yan ta'adda masu yaki da gwamnatin Siriya, Le Drian ya ce har yanzu shugaba Asad bai samu nasara na tabbatar da sulhu a kasar Siriya ba.
Yayin da ya koma kan halin da jahar Idlib ke ciki, Le Drien ya bayyana damuwarsa kan yiyuwar amfani da makamai masu guba, inda ya ce gwamnatin Faransa na tattaunawa da kasashen Rasha da Turkiya domin kaucewa wannan ibla'i. sannan kuma ya ce ko da gwamnatin Siriya ta kwace jahar Idlib daga hanun 'yan ta'adda ba za ta iya magance matsalar da yakin ya janyowa kasar ba.