Kayayyakin Abinci Na Halal Na Samun Karbuwa A Kasashen Turai
(last modified Fri, 28 Sep 2018 06:20:00 GMT )
Sep 28, 2018 06:20 UTC
  • Kayayyakin Abinci Na Halal Na Samun Karbuwa A Kasashen Turai

Kayayyakin Halal da ake sayarwa a kasashen turai na samun karbuwa daga al’ummomin kasashen.

Shafin yada labarai na Al-akhbar ya bayar da rahoton cewa, tun daga lokacin da aka fara sayar da kayan abinci masu lasisin halal a cikin kasashen turai da sauran kasashen duniya a cikin shekaru 1980, ya zuwa yanzu lamarin ya bunkasa fiye da kowane lokaci a baya.

Kayan abincin Halal dai sun hada da nau’oin nama, lemu kwalba da na gwangwani, madara da sauransu, har ma da kayan shafe-shafe na mata wadanda ba a gauraya su da abubuwan da aka haramta a musulunci ba, kamar giya ko naman alade.

Baya ga musulmi da suke zaune a kasashen turai ko kasashen da ban a musulmi ba, wasu mabiya addinai na daban na yin amfani da kayan abincin halal, inda suke bayyana cewa yana da inganci da kuma sauki idan aka kwatanta da na sauran kamfanoni.

Yanzu haka dai hannun jarin kamfanonin da suke samar da kayan abincin Halal yah aura dala biliyan 22.