MDD : Guterres Ya Bukaci A Tsawaita Aikin Tawagar Minurso
Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci a tsawaita aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, ta (Minurso) a yankin yammacin sahara.
A wani rahoto da Mista Guteres ya aikewa kwamitin tsaro na MDD a wannan mako, ya bukaci da a tsawaita aikin tawagar ta (Minurso) da shekara guda, domin karfafa farfado da tattaunawar siyasa da za'ayi tsakanin 'yan Polisario da kuma mahukuntan Marocco a farkon watan Disamba mai zuwa a Genava.
Mista Guteres ya ce ya bukaci hakan ne don baiwa wakilinsa na musamman isashen lokaci na shirya tattaunawar.
Sakatare janar na MDD, ya kuma neni wadanda batun ya shafa da kuma makobtansu dasu shiga tattaunawar da kyakyawar niyya.
tuni dai kasashen Aljeriya da Mauritaniya suka bayyana anniyarsu ta shiga tsakani a tattaunawar.
Marabin dai gwamnatin Marocco da 'yan Polisario su zauna teburin tattaunawa tun shekara 2012.