Halin Da Ake Ciki Kan Bacewar Dan Jarida Kashoggi
(last modified Thu, 11 Oct 2018 05:57:02 GMT )
Oct 11, 2018 05:57 UTC
  • Dan jaridar Saudiyyar Khashoggi ya bata a ranar 2 ga watan Oktoba 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya na Santambul
    Dan jaridar Saudiyyar Khashoggi ya bata a ranar 2 ga watan Oktoba 2018 a ofishin jakadancin Saudiyya na Santambul

A halin da ake ciki dai jami'an tsaron Turkiyya sun nuna hoton bidiyo na wasu jami'an Saudiyya da suka zo Turkiya a ranar da Jamal Khashoggi din ya bace.

Kafofin yada labarai a Turkiyya sun nuna hotunan jami'an su 15 wadanda sun isa birnin Santanbul cikin jiragen sama kirar Jet guda biyu.

Jami'an sun kuma yi rejista a otel, kuma a ranar sun shiga karamin ofishin jakadancin na Saudiyya, bayan shigar dan jaridan Jamal Gashoggi, bayan sa'oi biyu kuma suka fito suka bar kasar Turkiyya basu ma kwana a Otel din ba.

Hotunan bidiyon sun nuna lokacin da Kashoggi ya shiga ofishin, da kuma lokacin da suma jami'an suka shiga wurin a ranar 2 ga watan Oktoba nan.

Jami'an tsaro Turkiyya sun nuna hotuna da sunayen jami'an Saudiyyar su 15 ciki harda wani laftana kanal mai suna Salah Muhammed Al-Tubaigy, na sashen likitoci.

Shi dai Kashoggi din ya je ofishin ne bisa gayyata ofishin jakadancin kasarsa, kan bukatarsa ta kammala wasu takardun rabuwar aurensa, a shirye shiryen da yake na auren budurwarsa 'yar asalin kasar Turkiyya da suka je ofishin tare, amma ta jira shi a waje, kuma tun lokacin ba'a kara jin duriyarsa ba.

Wasu hotunan bidiyan sun nuno wata mota data shiga ofishin a lokacin, ta fito ta kuma je gidan karamin jakadan na Saudiyya dake kusa wurin ta kuma dawo ofishin.

Sakamakon farko na binciken da 'yan sandan kasar Turkiyya suka gudanar kan bacewar fitaccen dan jaridar Saudiyyar  Jamal Khashoggi mai sukar gwamnati, na nuni da cewa, an kasheshi ne a cikin karamin ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya da ke Satanbul kana aka fita da gawarsa aka jefar da ita,  sai dai Saudiyya ta musanta cewa tana da masaniya kan makomarsa, amma ta amsa cewa ya ziyarci ofishin nata a ranar Talata domin karbar wasu takardu, kuma ya fita bayan wani lokaci, saidai ta kasa tabbatar da yadda ya fita ofishin.

Bayannan da suka daurewa duniya kai su ne, yadda Saudiyya ta ce na'urori nadar hotuna da ke ofishin basa aiki, sannan kuma ta bada hutu haka kwatsam ga masu gadi 'yan kasar Turkiya a ranar da wannan lamari ya auku. 

Wannan al'amari dai ya sanya Saudiyya cikin tsaka mai wuya, Shugaban Turkiyya Receb Teyyib Erdogan ya bukaci Saudiyya data tabbatar da fitar dan jaridan daga ofishin.

Shugaban Amurka Donald Tromp wanda ya fara sanya baki a batun a baya bayan nan ya ce lamarin baida dadin ji, kuma a yanzu haka yana kan tattaunawa da mahukuntan koli na Saudiyyar, kuma ya tattauna da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohamed Ben Salam akan ya yi bayyani kan abunda ke faruwa. 

A nasu bangare 'yan majalisar datawan Amurka sun sha alwashin daukar matakan ladabtarwa idan dai har kisan gillan Kashoggi din ta tabbata.

A wani labarin kuma Jaridar Washigton Post, ta ce jami'an leken asirin Amurka sun cafko wata hira daga jami'an Saudiyya kan batun sace Kashoggi, duk da cewa gwamnatin Amurka ta musunta hakan.

Wannan al'amari dai da yafi karkata kan kisan gilla, zai iya kasancewa babban kalubale ga dankatar dake tsakanin Amurka da kawarta Saudiyya.