Kasar Venezuella Ta Soke Amfani Da Dalar Amurka
mataimakin shugaban kasar ta Venezuella Tareck El Aissami ne ya sanar da sabon matakin na daina amfani da kudin Amurka a mu'alar cinikayya da kasashen waje
El Aissami ya ci gaba da cewa; kasar Venezuella za ta maye gurbin dalar Amurka da kudin kasashen turai, Euro da kuma wasu kudaden masu daraja na duniya.
Mataimakin shugaban kasar ta Venezuella ya kuma ce; ba da jimawa ba gwamnati za ta zuba euro biliyan biyu a cikin kasuwannin kudaden na aksar.
Kasar Amurka dai tana amfani da kudinta na dala a matsayin wani makamin matsin lamba akan kasashen da ba ta ga maciji da su.
A cikin watannin bayan nan kasar ta Venezuella ta fuskanci tashe-tashen hanakli da 'yan hamayyar siyasa suke jagoranta. Kasar Amurka da kawayenta a yankin suna kokarin kifar da gwamnatin Nichols Maduro ta hanayr taimakawa 'yan hamayya da kuma kakaba takunkumai akan gwmanatin kasar.