Gwamnatin Pakistan Ta Saki Wani Komandan Kungiyar Taliban Bisa Bukatar Amurka
(last modified Thu, 25 Oct 2018 19:06:48 GMT )
Oct 25, 2018 19:06 UTC
  • Gwamnatin Pakistan Ta Saki Wani Komandan Kungiyar Taliban Bisa Bukatar Amurka

Gwamnatin Kasar Pakistan ta saki wani babban komanda kungiyar Taliban wanda take tsare da shi tun shekara ta 2010 bisa bukatar kasar Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Pakistan ta saki Mullah Baradar daya daga cikin manya manyan komandojin kungiyar taliban basi bukatar gwamnatin Amurka kuma a matsayin sharadi na tattaunawan da take yi da kungiyar.

Mullah Abdul Ghani Baradar tsohon na hannun damar shugaban kungiyar Taliban kuma wanda ya kafata wato Mullah Umar ne. Mullah Baradar yana tsare a hannun gwamnatin kasar Pakistan fiye da shekru 8 da suka gabata bayan wani sumamen da jami'an tsaron kasar Pakistan suka kaiwa mabuyarsa a birnin Karachi a shekara ta 2010..

Majiyar gwamnatin kasar Pakistan ta tabbatar da labarin sakin Mullah Baradar da ma wasu 'ya'yan kungiyar ta Taliban a cikin makonni biyu da suka gabata.

A ranar 12 ga watan Octoban da ya gabata ne wakilin gwamnatin Amurka  Zalmay Khalilzad ya gana, a asirce, da wasu wakilan kungiyar Taliban a birnin Doha na kasar Qatar, a wani shiri da suka kira tattaunawa da kungiyar ta Taliban. 

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa labarin a kafar sadarwa ta WattsApp.