Oct 26, 2018 05:49 UTC
  • Putin: Rasha Za Ta Kera Sabbin Makamai Marasa Tamka A Duniya

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewar kasarsa tana shirin kera wasu sabbin makamai wadanda ba su da tamka a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radio da Talabijin na Iran ya ba da rahoton cewa shugaba Putin ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a jiya Alhamis yayin wata ganawa da yayi da manyan kwamandojin sojin Rashan inda ya ce kasar Rasha za ta ci gaba da sabunta rumbunan makamanta, yana mai cewa kasar za ta kera sabbin makaman da babu irin su a duniya.

Shugaban na Rasha ya ci gaba da cewa kasar Rasha ba tana barazana ga wata kasa ba ce, sai dai za ta yi hakan ne don kare kanta daga duk wata barazanar da za ta iya fuskanta.

Shugaban na Rasha dai yana mayar da martani ne ga ikirarin shugaban Amurka Donald Trump wanda ya ce Amurkan za ta fice daga yarjejeniyar dakatar da kera makaman nukiliya tsakaninta da Rasha saboda abin da ya kira karya yarjejeniyar da Rashan ta yi.

Tags