Nov 29, 2018 17:47 UTC
  • Janar Hajizadeh: Iran Ta Kai Matsayin Sayar Da Makaman Da Ta Kera Zuwa Waje

Kwamandan dakarun kare sararin samaniyya na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh ya bayyana cewar a halin yanzu Iran ta kami matsayin sayar da makaman da ta kera zuwa kasashen duniya.

Kafar watsa labaran Sepah News ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na  Iran din ya bayyana cewar Birgediya Janar Hajizadeh ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gudanar wajen wani taro na dakarun kare juyin da aka gudanar a nan Tehran, babban birnin kasar Iran inda yayin da yake magana kan yadda Iran ta mayar da irin matsin lambar da aka mata ya zama wata dama ta ciyar da kasar gaba, ya ce: A halin yanzu Iran ta kai matsayin dogoro da kanta wajen kera makaman kare kanta, har ma za ta iya sayar da makaman ga kasashen da suke bukata.

Janar Hajizadeh ya ci gaba da cewa takunkumin zalunci da makiya suka sanya wa Iran ya zamanto wata dama ga kasar wajen dogaro da kanta da kuma irin karfi na cikin gida da take da shi.

Janar Hajizadeh ya bayyana cewar dalilin kiyayyar da Amurka take yi da Iran shi ne gabar da take yi da addinin Musulunci, don haka sai ya ce: Tsawon shekaru 40 din da suka gabata Amurka take kiyayya da Iran sai dai kawai hanyoyi da dabarun wannan kiyayyar ce watakila suke sauyawa.

Tags