Nov 25, 2018 11:52 UTC
  • Jamus Ta Dakatar Da Aikewa Saudiyya Makamai

Kamfanonin kera makamai na kasar Jamus sun jingire da aikewa Saudiyya makamai bayan da kasar ta haramta cinikin makamai da Saudiyya

Tashar tabalijin din aljazeera ta ba da labarin da yake cewa; Bayan kisan da aka yi wa dan jaridar Saudiyya Jamal Kashoogi, kamfanonin kera makamai na kasar Jamus sun sanar da dakatar da aike wa Saudiyyar makamai har zuwa shekarar 2019 mai zuwa

Bugu da kari ma'aikatar harkokin wajen kasar Jamus ta sanar da kakaba takunkumin tafiya akan wasu 'yan Saudiyya 18 da hana su shiga cikin kasarta.

An kashe Jamal Kashoogi ne dai a ranar 2 ga watan Oktoba da ya shiga cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya. Sai bayan gushewar kwanaki 18 ne sannan Saudiyyar ta yi furuci da kashe Kashoogin saboda matsin lamabar da ta fuskanta daga kasashen duniya.

Kasar Jamus da wasu kasashen turai sun kakaba wa Saudiyyar takunkumin sayar mata da makamai.

Tags