Korea Ta Arewa Ta Sake Sabin Kwajin Makamai
(last modified Fri, 16 Nov 2018 19:06:00 GMT )
Nov 16, 2018 19:06 UTC
  • Korea Ta Arewa Ta Sake Sabin Kwajin Makamai

A wannan juma’a shugaban Koriya ta Arewa ya jagoranci bikin kaddamar da wasu sabbin makaman yaki da ake ganin cewa zai sa a diga ayar tambaya dangane da shirin kasar na kwance wa kanta damarar nukiliya.

Kafar yada labaran Koriya ta Arewa ta habarta cewa a yau juma'a shugaban kasar Kim Jong Un ya jagoranci wani sabon kwaji na makami mai Linzami, inda ya bayyana gamsuwarsa da nasarar da aka samu, sannan kuma ya ce sabon makamin, zai sake tsaurara tsaro da kuma karfafa sojojin kasar. Shugaba Kim ya bayyana jin dadinsa matuka kan gwajin da ya ce ya cimma bukatunsu.

A yan watanni da suka gabata a lokacin shiga tattaunawa da Koriya ta kudu da Amurka ma’aikatar leken asirin kasar Amurka ta bayyana matukar damuwarta, inda ta ce yanzu haka kasar Koriya ta arewa na ci gaba da kera wasu sabbin makamai masu linzame dake cin zangon kasa da kasa

Ba sabon abu bane kasar Koriyar ta arewa ta furta cewa, tana iya kera makaman da zai iya cin dogon zangon da zai kai ga kasar Amruka