Jami'ar Siyasar Waje Ta Turai Tana Adawa Da Kafa Rundunar Soja
Babbr jami'a mai kula da siyasar waje da kuma tsaro ta turai Fredrica Murghnai ta nuna adawarta da kafa rundunar soja ta nahiyar turai
Jami'ar ta ce; Tarayyar turai ba kawance ne na soja ba, kuma ba zai taba zama hakan ba.
Jawabin na Fredrica Mughrani ya zo ne kwanaki kadan bayan da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kira da a kafa rundunar soja ta tarayyar turai, abinda shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta nuna goyon baya akai.
Mughrani wacce ta gabatar da taron manema labaru jiya a cibiyar tarayyar turai, da ke Brussels ta ce; " Tarayyar turai ba za ta taba sauyawa zuwa wani kawance na soja ba, domin ba ta gasa da yarjejeniyar tsaro ta Nato.
Murghani ta kuma ce; Tarayar turai an yi ne domin samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin yakin kuma tana zuba hannun jari a cikin ko'ina a duniya, amma duk da haka ba za ta kafa rundunar soja ba."
Kasar Amurka na cikin na farko-farko da su ka mayar wa da shugaban kasar Faransa martani akan kiran nasa na kasa rundunar soja ta tarayyar turai kadai.