Nov 27, 2018 06:43 UTC
  • Kasar Jamus Na Son Ganin An Yi Wa Kwamitin Tsaro Kwaskwarima

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas ne ya bayyana cewa: Al'murran duniya sun shiga cikin rudadin da tsarin kwamitin tsaro na yanzu ba zai iya warware shi ba

Maas ya kara da cewa; Tamkar sauran kasashe irin su Japan da Indiya muna yin tunanin hanyoyin da za a rika daukar matakai na bai daya

A shekara mai zuwa ne dai kasar ta Jamus za ta shiga kwamitin tsaro domin zama memba na tsawon shekaru biyu a jere.

Bugu da kari ministan harkokin wajen kasar ta Jamus ya kira yi sauran kasashen turai da su yi aiki tare domin ganin sun cimma manufofin da su ka sanya a gaba, daga ciki hadda batun kasuwanci da kuma yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Tun a cikin shekarar 1993 ne aka fara yin kira da samar da sauyi a cikin tsarin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. A halin yanzu kwamtin yana da dawwamammun mamabobi 5 da kuma wasu 10 na wucin gadi.

Tags