Venezuela : Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi
(last modified Mon, 10 Dec 2018 10:41:13 GMT )
Dec 10, 2018 10:41 UTC
  • Venezuela : Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi

Jam'iyyar mai mulki ta Shugaba Nicolas Maduro a Venezuela, ta lashe da gagarimin rinjaye zaben kananen hukumomi na kasar.

A sakamakon da hukumar zaben kasar ta (CNE) ta fitar, Jam'iyyar 'yan gurguzun ta (PSUV), ta lashe majalisun kananan hukumomi 142 daga cikin 156.

Har yanzu 'yan adawa na riki da kashi guda cikin hudu na kananan hukumomi 335 na kasar ta Venezuela. 

Shugaba Nicolas Maduro dai na zargin shuwagabannin kasashen yamma ciki har da Donald Trump da yi masa makarkashiya domin kifar da mulkinsa.