Birtaniya Ta Yi Gargadi Akan Sake Dawowar Kungiyar Alka'ida
Jami'i mai kula da harkokin tsaro a Maikatar harkokin cikin gidan Birtaniya Ben Wallace ya ce; Kungiyar alka'ida tana da niyyar kai wasu sabbin hare-hare akan filaye jiragen sama a nahiyar turai
Jami'in tsaron na Birtaniya ya ce bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu kungiyar ta dukufa wajen lakantar harkar injiyanci domin iya kakkabe da jiragen sama na fasinja
Wallace ya kuma bayyana cewa; Daga cikin abubuwan da alka'ida ta mayar da hankali akansa a halin yanzu take aiki akansa, da akwai jirgin maras matuki da kuma yadda a yi amfani da shi wajen kai hare-hare
Kwanaki uku ajere an rufe filin saukar jiragen sama na Gatwicg na Birtaniya saboda shawagin da jirage marasa matuki su ka yi kusa da shi, lamabari da ya zama barazana ga lafiyar sufurin sama