Siriya : Rasha Da Turkiyya Zasuyi Hadin Gwiwa Bayan Janjewar Amurka
Kasashen Rasha da Turkiyya, sun bayyana anniyarsu ta yin aiki tare a Siriya, biyo bayan matakin Amurka na janye dakarunta daga Siriya.
Wata sanarwa da bangarorin biyu suka fitar a wata tattaunawa a Moscow, sun ce zasuyi hadin gwiwa a fagen daga da zumar kawar da barazanar 'yan ta'adda a Siriya.
Da yake karin bayyani dangane da tattaunawar, ministan harkokin wajen Rasha Sergueï Lavrov, ya ce sun tattauna da takwaransa na Turkiyya Mevlüt Cavusoglu, kan yadda zasu aiki tare biyo matakin na Amurka na sanar da janye sojojinta daga Siriya.
Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi tattaunawar ce tare da halartar ministocinb tsaron kasashensu.
Tattaunawar dai na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da shirin janye sojojin kasarsa daga Siriya.
Da yake bayyani shi ma kan tattaunawar ministan harkokin wajen Turkiyya, Cavusoglu, ya ce bangarorin biyu zasuyi aiki tare da kawayensu Rasha da Iran domin gaggauta shirin tattaunawar neman sulhu ta hanyar siyasa domin samun mafita kan rikicin Siriya.
Kasashen na Turkiyya da Rasha, sun kuma sha alwashin taimakawa wajen ganin 'yan gudun hijira Siriya sun koma gidajensu, tare da basu tallafin jin kai, da kuma zurfafa yin aiki tare na samar da tuddan mun tsira a Idleb, yanki na karshe daka hannun 'yan tada kayar baya.
Nan gaba a farkon shekarar 2019 mai shirin kamawa ne ake sa ran shugabannin kasashen Iran, Turkiyya da kuma Rasha zasuyi wani taro kan batun na Siriya a cewar mahuuntan Moscos.