Lavrov: Shekara Ta 2018 Shekara Ce Mai Tsanani Ga Kasar Rasha.
(last modified Tue, 01 Jan 2019 06:51:18 GMT )
Jan 01, 2019 06:51 UTC
  • Lavrov: Shekara Ta 2018 Shekara Ce Mai Tsanani Ga Kasar Rasha.

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sargai Lavrov ya bayyana cewa shekara ta 2018 da ta shude , shekara ce mai tsanani ga kasar Rasha.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin waje na kasar Rasha yana fadar haka a jawabinsa na shigowar sabowar shekara ta 2019 a jiya da dare.

Lavrov ya kara da cewa mafi tsananin takurawa da kasar Rasha ta fuskanta a shekara da ta gabata daga kasar Amurka ne, sannan kasashen Turai ma sun biyewa Amurka hatta a wuraren da suma zasu cutu, ko kuma ba maslaharsu bane .

Minisyan ya kara da cewa wani abin bakin ciki a shekara da ta gabata shi ne yin watsi da bukatar kasar Rasha batun yerjejeniyar Makamai masu linzami masu daular makaman nukliya wanda kasar Rasha ta gabatarwa komitin tsaro na MDD. Lavrov ya ce a nan ma kasashen turai sun biyewa kasar Amurka duk da cewa yerjejeniyar tana da muhimmanci a garesu.

Daga karshe ministan ya bayyana cewa akwai fatan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai hadu da tokoransa na kasar Amurka Donal Trimp don tattauna wannan batun a cikin wannanan shekarar. Ya kuma kara jaddada bukatar a tattauna wannan batun don muhimmancinsa.