An Yi Allahwadai Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar Venezuela.
Yan siyasa a kasar Faransa da wasu manya-manyan kasashen duniya sun yi allawadai da kokarin juyin mulki a kasar Venezuela.
Kamfanin dillancinn labarann Spotnicts ta nakalto Jean-Luc Mélenchon, da kuma Éric Coquerel fitattukan yan siyasa na jam'iyyar adawa na jam'iyyar "Incompatible" suna tir da kokarin juyin mulki a kasar Venezuela.
Fadar Elize a birnin Paris dai ta ce tana bin yadda al-amura suka faryuwa a kasar Venezuela , kuma zata bayyana matsayinta bayan ta shawarci kawayenta na kasashen Turai.
A jiya Laraba ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana goyon bayansa ga yan adawa a kasar Venezuela, kuma ya bukaci shugaban kasar Nicola Badoru da ya sauka kan kujerar shugabancin kasar ya kuma mika mulki ga yan adawar ksar.
A maida martani shugaban kasar ta Venezuela ya bayyana katse dangantakar kasar Venezuela da Amurka, ya kuma bawa jami'an diblomasiyyar kasar Amurka a Caracas sa'o'i su bar kasar.
Kafin haka dai shugaban wata jam'iyyar adawa ta kasar Venezuela Juan Guaido ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasar Venezuela.
A halin yanzu dai masu goyon bayan gwamnati da kuma yan adawa suna ta fafatawa a kan titunan kasar .