Venezuela : Sojoji Sun Nuna Goyan Baya Ga Maduro
(last modified Fri, 25 Jan 2019 03:48:28 GMT )
Jan 25, 2019 03:48 UTC
  • Venezuela : Sojoji Sun Nuna Goyan Baya Ga Maduro

Sojoji a Venezuela, sun nuna goyan bayansu ga shugaban kasar, Nicolas Maduro, a daidai lokacinda wasu manyan kasashen duniya a sahun gaba Amurka suka bayyana goya baya ga shugaban majalisar dokokin Venezuelar da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na wucin gadi.

A wani taron manema labarai a Caracas, ministan tsaron kasar, Janar Vladimir Padrino, kewaye da manya manya hafsoshin sojin kasar sun yi tir da allawadai da abunda suka danganta da juyin mulki daga shugaban majalisar dokokin kasar.

Ministan tsaron kasar, ya kuma ce, yana mai ja hankalin 'yan kasar ta Venezuela, cewa ''ana yunkurin juyin mulki wa manyan cibiyoyin gwamnati, da demokuradiyya da kundin tsarin mulki da kuma halastacen shugaban kasarmu, Nicolas Maduro''.

Ko baya ga sojojin kasar shugaba Maduro na samun goyan bayan wasu manyan kasashen duniya da suka hada da Chine, Turkiyya, Mexico da kuma Rasha.

Kasashen dai sunyi allawadai da tsoma baki na AMurka a cikin al'amuran cikin gida na kasar ta Venezuela.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin wanda ya nuna goyan bayansa ga halataccen shugaban kasar ta Venezuella, ya ce rikicin siyasa na Venezuella, nada nasaba da sanya hannu na wasu kasashen waje, a sahun gaba Amurka, wanda kuma hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.

A ranar Litini dai an dakile yunkurin wasu sojojin venezuella na juyin mulki.