Venezuella Ta Yi Watsi Da Wa'adin Kasashen Turai Na Kiran Zabe
(last modified Sun, 27 Jan 2019 11:03:23 GMT )
Jan 27, 2019 11:03 UTC
  • Venezuella Ta Yi Watsi Da Wa'adin Kasashen Turai Na Kiran Zabe

Kasar Venezuella ta yi watsi da wa'addin da wasu kasashen turai suka bata na ta kira zabe cikin kwanaki takwas ko kuma su amince da jagoran 'yan adawa na kasar a matsyin shugaban riko na kasar.

Ministan harkokin wajen kasar ta Venezuella, Jorge Arreaza, ya ce, babu wani mahaluki da ya isa ya gindaya masu wani wa'adi, balle ma ya gaya mana mu kira zabe ko kuma a'a.

Mista Arreaza, ya danganta wannan da wani shishigi a cikin al'amurran cikin gidan kasar ta Venezuella.

A jiya ne wasu kasashen turai da suka hada da  Faransa, Jamus da Spain suka baiwa Shugaban kasar ta Venezuela, Nicolas Maduro, wa'adin kwanaki takwas na ya kira zabe ko kuma su amince da jagoran 'yan adawa na kasar, Juan Guaido a matsayin shugaban riko na kasar wanda zai shirya zabubuka nan gaba.