An Bukaci Hana Juan Guaido Fita Venezuela
Babban mai shigar da kara na gwamnatin Venezuela, ya bukaci kotun kolin kasar data haramta wa jagoran 'yan adawa na kasar Juan Guaido fita kasar da kuma toshe asusunsa na banki.
Da yake sanar da hakan, mai shigar da kara na gwamnatin ta Venezuela, Tarek William Saab, ya ce, an bude bincike kan Mista Guaido, a don haka ya ce a rufe asusunsa da kuma hana shi fita kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskanta takun tsaka tsakanin gwamnatin ta Venezuela da kuma Amurka, wacce ta amince da jagoran 'yan adawan Venezuela a matsayin halattacen shugaba, tare da sanar da kakaba sabbin takunkumai kan kasar ta Venezuela, wanda suka shafi fannin man fetur.
Kafin hakan dai shi Shugaba Nicilas Maduro, ya dora alhakin dukkan zubar jinin da zai faruwa a kasar ga Shugaba Donald Trump na Amurka.