Turai Na Shirin Bayyana Goyon Bayanta Ga Juyin Mulki A Venezuela
(last modified Sat, 02 Feb 2019 07:17:42 GMT )
Feb 02, 2019 07:17 UTC
  • Turai Na Shirin Bayyana Goyon Bayanta Ga Juyin Mulki A Venezuela

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya sanar a daren jiya juma'a cewa kasashe 28 na kungiyar tarayyar Turai sun yanke shawarar ko wata kasa daga cikin manbobinta ta bayyana goyon bayanta ga Juan Guaido shugaban 'yan adawar kasar Venezula a matsayin shugaban kasa ficin gadi.

Rahoton ya ce kasashen na Turai sun kudiri cewa a maimakon bayar da sanarwar hadin gwiwa, ko wata kasa ta bayyana goyon bayanta ga Juan Guaido.

A ranar akhamis din da ta gabata ce 'yan majalisun kasashen Turai suka jefa kuri'a amincewa da Juan Guaido a matsayin shugaban kasar Venezuela na rikin gwarya, bayan wannan mataki Majalisar ta bukaci ko wata kasar ta yi aiki da wanan umarni.

A ranar 23 ga watan janairun da ya gabata ne dai shugaban Majalisar dokokin kasar ta Venezuela Juan Guaido ya shelanta kansa a matsayin shugaban kasar, lamarin da ya bude sabon shafin dambaruwar siyasa a cikin kasar

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da ministansa na harkokin wajen Mike Pampeo da wasu kasashen Turai da suka hada da kasar Faransa sun nuna cikakken goyon bayansu ga Juan Guaido tare da daukarsa a matsayin shugaban kasa.

Saidai a bagare guda, kasashen Rasha da China, da jamhoriyar musulinci ta Iran gami da wasu kasashen Afirka sun nuna goyon bayansu ga shugaba mai ci Nicolas Maduro.