Turkiyya : Erdogan Ya Zargi (EU), Da Kokarin Kifar Da Gwamnatin Venezuela
(last modified Tue, 05 Feb 2019 16:11:14 GMT )
Feb 05, 2019 16:11 UTC
  • Turkiyya : Erdogan Ya Zargi (EU), Da Kokarin Kifar Da Gwamnatin Venezuela

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya zargi kungiyar tarraya Turai ta (EU), da kokarin kifar da gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela.

Da yake bayyana hakan a wani jawabi ta gidan talabijin, shugaba Erdogan, yanzu mun riga mun san wacce EU, a hannu guda kuna batun zabe da kuma demokuradiyya, amma daga baya ta hanyar rikici zaku kifar da gwamnati.

Mista Erdogan na maida martani ne kan kasashen turan da suka amince da jagoran 'yan adawa na kasar Venezuela, Juan Guado, a matsayin shugaban riko na kasar.

A farkon makon nan ne wa'adin kwanaki takwas da kasashen turan da suka hada da Faransa, Jamus, Spaniya, Buritaniya, Portigal, gami da Austria, suka dibarwa shugaba Maduro ya kawo karshe.

Shugaba Maduro, dai ya yi watsi da wa'adin da kasashen turan suka dibar masa na shirya sabon zabe shugaban kasa.

Kasashen Rasha, China, Turkiyya, da Iran na zargin kasashen turan da kuma Amurka, da shishigi a cikin al'amuran cikin gida na Venezuela.