Venezuela Ta Yi Allawadai Da Yi Mata Kutse
(last modified Fri, 08 Feb 2019 04:26:55 GMT )
Feb 08, 2019 04:26 UTC
  • Venezuela Ta Yi Allawadai Da Yi Mata Kutse

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Venezuela, ta sanar da yi mata kuste a shafukan intarnet na ofisohin jakadancinta na Mexico da Argentina, inda aka wallafa sakwannin nuna goyan baya ga madugun 'yan adawa na Venezuela wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar.

A cikin sanarwar data fitar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Venezuela, ta karyata labarin, tana mai kuma allawadai da irin wannan salo na yi mata kutse, wanda ta danganta da tsatsauran ra'ayi na siyasa, na neman kifar da shugaban kasar Nicolas Maduro. 

Dama kafin hakan an wallafa irin wannan sako, a shafukan intanet na ofisohin jakadancin kasar na Brazil, da Canada, da Columbia, da Rasha, da Uruguay da Guatemala da Italiya, da masar da Costa Rica.

Jekadiyyar Mexico a Mexico, Maria Lourdes Urbaneja, ita ma tayi allawadai da kutsen da akayi wa ofishin nata, inda a cikin wani sakon faifan bidiyo ta jadadda goyan bayanta ga shugaba Maduro.