MDD:Ta Dora Alhakin Kisan Khashoggi Kan Mahukuntan Saudiya
Masu binciken MDD na musaman kan kisan Jamal Khashoggi sun gabatar da rahoto wanda ya dora alhakin kisan kai tsaye ga mahukuntan kasar Saudiya
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Agnès Callamard shugaban tawagar gudanar da bincike kan kisan da aka aiwatar a kan shahararen dan jaridar nan na kasar Saudiya Jamal Khashoggi a jiya alhamis na cewa wannan kisa abu ne da mahukuntar kasar Saudiya suka shirya shi a baya sannan suka aiwatar da shi a karamin ofishin jakadancin kasar dake birnin Istambul na kasar Turkiya.
Rahoton farko ya sannan da cewa mahukuntar birnin Riyyad sun iya kokarinsu na ganin raunana binciken da gwamnatin kasar turkiya ta gudanar.
Jamal Khashoggi dan jarida ne da ya kasance yana sukan manufofin gwamnatin kasar Saudiya, a ranar Talata 2 ga watan Oktobar shekarar 2018 din da ta gabata ya yi batan dabo bayan da ya shiga karamin ofishin jakadancin kasar Saudiya dake birnin Istambul na kasar Turkiya.
Bayan karyata kisan da ta aiwatar, a ranar 19 ga watan Oktaba, mahukuntar kasar Saudiya sun amince da kisan Jamal Khashoggi bayan matsin lambar da suka fuskanta daga kungiyoyin kasa da kasa.
Kafin hakan dai Jamal Khashoggi ya kasance daga cikin mutanan da gwamnatin saudiya ke nema ruwa a jalo, inda ya fice daga cikin kasar yana rayuwa a kasar Turkiya.