Dakarun tsaron Jamus za su fadada aiyukansu a Mali
Kasar Jamus ta ce za ta fadada aiyukan soja a Kasar Mali
A yayin ziyarar aikin da ya kai kasar Mali jiya Laraba Ministan harakokin tsaron Jamus ya bayyana cewa kasar sa za ta kara yawan aiyukan sojan da take yi a kasar tare kuma da kara bayar da horo kan dakarunsu dake gariruwan arewacin Mali kan yadda za su tunkari 'yan tawaye masu tsaurin ra'ayi.
A Maku mai kamawa, Ministan ya ce zai a jiye wata bukata a gaban Majalisar dokokin kasar sa domin gudanar da canje-canjen da suka dace a dakarun tsaron kasar dake kasar ta Mali.
Rahoton ya ce nan gaba kasar ta jamus za ta tura Dakaru kimanin 600 a kasar ta Mali domin bayar da horo tare kuma da taimakawa kasar a yayin da ta yi da masu tayar da kayar baya.