Rasha Da Cana Suna Goyon Bayan Maduro Na Kasar Venezuela
(last modified Fri, 22 Feb 2019 19:07:01 GMT )
Feb 22, 2019 19:07 UTC
  • Rasha Da Cana Suna Goyon Bayan Maduro Na Kasar Venezuela

Kasashen Rasha da Cana suna goyon bayan shugaban kasar Venezuela Nicola Maduro a dai-dai lokacinda Amurka tana son ta farwa kasar da yaki.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana son ta shigar da abinda ta kira taimako cikin kasar ta Venezuela da karfi. 

Kasashen Rasha ta cana dai dai sun nuna rashin amincewarsu da duk wani harin da Amurka zata kaiwa halattaciyar gwamnatin kasar Venezuela..

 A jiya Alhamis ne gwamnatin kasar ta Venezuela ta bada sanarwan rufi kan iyakokin kasar da kasar Brazil, sannan ta yi barazanar zata rufe kan iyakarta da kasar Colombiama, idan har shugaban yan adawar kasar Juan Guaido ya yi kokarin shigo da abinda suka kara taimako cikin kasar.

Ministan harkokin wajen kasar Cana ya ce bai kamata a ace sai an shigarda abinda aka kira taimako cikin kasar Venezuela da karfi ba. 

Kasashen biyu sun bayyana rashin amincewarsu da duk abinda zai jawo tashin hankali a kasar Venezuela.