Feb 27, 2019 18:24 UTC
  • Taliban Ta Gargadi India Dangane Da Ci Gaba Da Kai Wa Pakistan Hari

Kungiyar Taliban ta gargadi gwamnatin India dangane da ci gaba da kai wa kasar Pakistan hari, tare bayyana hakan a matsayin lamari mai matukar hadari.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fadi a yau cewa, idan har India ta ci gaba da kai wa Pakistan harin soji, to kuwa hakan zai haifar da matsaloli masu tarin yawa a yankin.

Ya ce daga cikin matsalolin da hakan zai haifar hard a yin mummunan tasiri ga tattaunawar sulhu da ake gudanarwa a kasar Afghanistan.

Gwamnatin kasar Pakistan ta bayyana cewa ta kakabo jiragen yakin kasar India guda biyu a cikin yankinta, kuma ta kame wani matukin jirgin sojin kasar India da ke tuka daya daga cikin jiragen.

A halin yanzu dai kasashen duniya suna ci gaba da yin kira ga kasashen biyu da su kai zuciya nesa, kuma su rungumi zaman lafiya da hakuri da juna.

 

 

 

 

 

 

 

 

Tags