Zanga-Zangar Kyamar Gwamnati A Ukraine
An gudanar da wata zanga-zanga a birnin Kiev fadar mulkin kasar Ukraine, domin sukar lamirin gwamnatin kasar kan batun cin hanci rashawa.
Rahotanni daga birnin an Kiev sun ce masu zanga-zangar sun yi cincirindo a gaban fadar shugaban kasar, inda suka yi ta rera taken sukar gwamnatin kasar, inda suke zargin jami'anta da cin hanci da rashawa, da hakan ya hada har da shugaban kasar Petro Poroshenko da kuma alkalin alkalan kasar Viktor Shokin .
Amma a nasa bangaren shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko ya musunta zargin da masu zanga-zangar suke yi a kansa da kuma jami'an gwamnatinsa.
Kafin isar masu zanga-zangar zuwa fadar shugaban kasar ta Ukrainea birnin Kiev, 'yan sanda sun yi amfani da kulake da hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa su, amma hakan bai iya hana su isa bakin fadar shugaban kasar ba.