Tarayyar Turai: Ukraine Ta Shiga Halin Rashin Tabbas
Shugaban majalisar kungiyar tarayyar turai ya fadi a yau cewa, tun bayan da fira ministan kasar Arseniy Yatsenyuk ya yi murabus, kasar ta kara shiga cikin wani hali na rashin tabbas.
Kamfanin dillancin labaran Reuters daga birnin Brussels ya bayar da rahoton cewa, Martin Schulz ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanatawa da manema labarai a babban ginin majalisar kungiyar tarayyar turai, inda ya ce halin da Ukraine ta shiga bababn abin bakin ciki ne ga dukkanin kasashen turai.
Kasashen yammacin turan dai sun raba kasar Ukraine da kasar Rasha wadda ke tallafa mata adukkanin bangarori tun daga shekara ta 2013, bisa cewa za su taimaka mata ta fuskar tattalin arziki fiye da Rasha, kuma za su mayar da ita mamba a kungiyar tarayyar turai, inda har yanzu ba ta samu taimakon nasu ba, kuma ba su mayar da ita mamba a kungiyar tarayyar turan ba.