Syria : Bashar Al'Assad Zai Ci Gaba Da Mulki
Apr 17, 2016 04:59 UTC
-
John Kerry da Sergio Lavrov
Amurka da Rasha sun cimma matsaya guda akan rikicin Syria, wace ta tanadi cewa Bashar Al'assad zai gaba da mulki, kana kuma ya tsaya takara a zaben shugaban kasa.
Kamar yadda wasu majiyoyin diflomatsiyan kasashen yamma dake bin diddigin tattaunawar da ake a Geneva suka shaidawa jaridar ''Asharq Al-Awsat'', sun ce kasashen biyu sun tattauna kan yadda za'a kafa gwamatin rikon kwarya a kasar ta Syria.
kuma bayan tattaunawar Amurka ta amunce da shawara Rasha kan batun gwamnatin rikon kwarya, dama yadda gwamnatin zata kasance da kundin tsarin mulkin da kuma batun zabubukan kasar da za'a gunanar nan da wattani 18.
Tags