UNHCR Na Fargaba Mutuwar Bakin Haure 500 A Teku
Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD, ta ce bakin haure akalla 500 ne ake kyautata zaton sun mutu sanadiyar hadarin da kwale-kwalen da suke ciki ya yi a tekun Mediterranean.
Bayanai sun nuna cewa kwale-kwalen ya yi hadari ne a 'yan kwanakin nan tsakanin kasashen Libya da Italiya.
Wasu daga cikin bakin hauren 41 da suka samu isa yankin Kalamata, dake kudu maso yammacin kasar Girka ne suka bayar da labarin da kuma alkalluman yawan mutanen.
Mafi yawa daga cikin bakin hauren ‘yan asalin kasashen Somalia da Sudan da kuma Habasha da kuma Masar ne.
Rayukan daruruwan bakin haure ne ke salwanta kusan kullum a tekun mediterrranean, yawanci wadanda ke tserewa yake-yake a kasashensu zuwa Nahiyar Turai.