Paparoma Francis Ya Bukaci Warware Rikicin Kasar Siriya Ta Hanyar Lumana
https://parstoday.ir/ha/news/world-i4687-paparoma_francis_ya_bukaci_warware_rikicin_kasar_siriya_ta_hanyar_lumana
Shugaban darikar Catholica ta mabiya addinin Kirista ta duniya ya bukaci warware rikicin kasar Siriya ta hanyar lumana.
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 03, 2016 01:06 UTC
  • Paparoma Francis Ya Bukaci Warware Rikicin Kasar Siriya Ta Hanyar Lumana

Shugaban darikar Catholica ta mabiya addinin Kirista ta duniya ya bukaci warware rikicin kasar Siriya ta hanyar lumana.

Paparoma Francis ya bayyana tsananin damuwarsa kan halin tsaka mai wuya da al'ummar Siriya suka shiga sakamakon bullar ayyukan ta'addanci a kasar yana mai fayyace cewa; Makircin makiya dan Adamtaka ya wurga kasar cikin halin tsaka mai wuya.

Paparoma Francis ya kuma jaddada bukatar ganin bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar ta Siriya sun hanzarta hauwa kan kujerar tattaunawa da nufin neman hanyar sulhuntawa domin kawo karshen rikicin kasar ta hanyar lumana.

Har ila yau Paparoma Francis ya jaddada wajabcin mutunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakanin gwamnatin Siriya da 'yan tawayen kasar.