Karshen Yakin Siriya Amfanin yanki da Duniya baki daya ne
Shugaban Kasar Siriya ya tabbatar da cewa samun nasara a kan 'yan ta'adda amfanin yanki da Duniya ne
A yayin wani jawabi da ya gabata yau Alkhamis, Shugaban Kasar Siriya Bashard Al-Assad ya jinjinawa Magabatan birnin Masco kan goyon bayan da suke baiwa Damuscus wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda, sannan ya ce Samun nasarar Siriya a kan 'yan ta'adda amfanin dukkanin kasashen yankin ne da ma Duniya baki daya.
Shugaba Asad ya kara da cewa matsayar da kasar Rasha ta dauka wajen taimakon Al'ummar Siriya da kuma tsayin daka wajen yakar 'yan ta'adda shine ke nuna kyakkyawar aniwar kasar na yaki da zalinci .
Yayin da yake ishara kan goyon bayan da kungiyoyin 'yan ta'addar ke samu daga wajen wasu manyan kasashen Duniya, Shugaba Asad ya ce babu wani kudiri da za mu amince da shi face fitar 'yan ta'adda daga cikin kasar mu.
Har ila yau Shugaban kasar ta Siriya ya bayyana kyakkyawan fatansa na samun nasarar karshe a yakin da kasar ke yi tare da kungiyoyin 'yan ta'adda, kuma hakan amfani ne ga Duniya baki daya.