MDD ta nada sabon Manzonta na musaman kan kasar Guinee Bisaou
May 08, 2016 07:38 UTC
Daftarin Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da nada Manzon Musaman da zai bi kadun zaman lafiya a kasar Guine Bisaou
Kafar watsa labaran Afirka time ta habarta cewa Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya nada Modibo Toure Dan kasar Mali a matsayin Sabon Manzon Majalisar kan Kasar Guinee Bissaou.
Shidai Modibo Toure shine wanda zai mayar gurbin Miguel Trovoada da wa'adin aikinsa ya kare a ranar 30 ga watan Avrilun da ya gabata.
Daftarin Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa Kafin wannan sabon matsayi, mista Modibbo Toure ya kasance mai baiwa Manzon musaman na MDD Shawara a yankin tabkin Tchadi a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015.
Tags