Jami'an Tsaron Tunusiya Sun Yi Nasarar Tarwatsa Wasu Gungun 'Yan Ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5056-jami'an_tsaron_tunusiya_sun_yi_nasarar_tarwatsa_wasu_gungun_'yan_ta'adda
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunusiya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wata kungiyar ta'addanci tare da tarwatsata a yankin kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:15+00:00 )
May 11, 2016 10:24 UTC
  • Jami'an Tsaron Tunusiya Sun Yi Nasarar Tarwatsa Wasu Gungun 'Yan Ta'adda

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunusiya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wata kungiyar ta'addanci tare da tarwatsata a yankin kudancin kasar.

A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunusiya ta fitar a yau Laraba yana dauke da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wasu gungun 'yan ta'adda a lardin Mahdiyya da ke kudancin kasar ta Tunusiya, inda suka kai farmaki tare da samun nasarar kame 'yan ta'addan.

Gungun 'yan ta'addan sun yi furuci da cewar suna aiki ne karkashin kungiyar ta'addanci ta Da'ish kuma ayyukansu sun takaita ne a fagen sada zumunta da nufin gurbata tunanin matasa.