An Shiga Halin Ko ta kwana A Kasar Venezuela
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5194-an_shiga_halin_ko_ta_kwana_a_kasar_venezuela
Shugaban Kasar Venezurla, Nicolas Maduro ya kafa dokar ta baci a kasar bisa zargin kokarin kifar da gwamnatinsa.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 14, 2016 15:12 UTC
  • An Shiga Halin Ko ta kwana A Kasar Venezuela

Shugaban Kasar Venezurla, Nicolas Maduro ya kafa dokar ta baci a kasar bisa zargin kokarin kifar da gwamnatinsa.

Shugaban na kasar Venezuela ya fadi cewa; Ina sanar da kafa halin ko ta kwana na tattalin arziki domin kare kasarmu.

Shugaba Maduro wanda ya rattaba hannu akan dokar da za ta sa a kafa halin ko ta kwana a cikin kasar ya kuma ce; Zai yi aiki da ikon da tsarin mulkin kasar ya bashi domin kare ta daga yakin tattalin arziki.

Tun a jiya juma'a ne dai shugaba Maduro ya ce; Da akwai makarkashiyar tattalin arziki da ake kitsawa kasarsa a cikin kungiyar Opec da kuma Amurka domin kifar da gwamnatinsu ta gurguzu.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan yadda dokar za ta yi aiki.