Venezuela : Za 'a Hukunta Kamfani Da Ya Dakatar Da Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5224-venezuela_za_'a_hukunta_kamfani_da_ya_dakatar_da_aiki
Shugaban kasar venezuela Nicolas Maduro ya bayyana Za' a hukunta duk wani kamfani ko ma'aikatar da ta dakatar da aiki a kasar da nifin kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 15, 2016 06:31 UTC
  • Venezuela : Za 'a Hukunta Kamfani Da Ya Dakatar Da Aiki

Shugaban kasar venezuela Nicolas Maduro ya bayyana Za' a hukunta duk wani kamfani ko ma'aikatar da ta dakatar da aiki a kasar da nifin kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.

Mr Maduro wanda ke bayyana hakan a wani jawabin da ya yi ga magoya bayansa, ya zargi masu masana'antun da yi wa gwamnatinsa zagon-kasa.

Don haka a cewarsa za' a garkame duk wanda aka samu da hannu a wannan yunkurin a babban gidan yarin kasar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasar ya kafa dokar-ta-baci domin dakile abin da ya bayyana da mamayar kasashen waje, wadanda a cewarsa su ne umal aba'isin hadasa tabarbarewa tattalin arzikin kasarsa.