An Kira yi Taliban Ta Afghanistan Da Ta Rungumi Zaman Lafiya
May 26, 2016 12:10 UTC
Shugaban Jam'iyyar Hizbul-Islami ta Afghanistan, Gulbaddin Hikmater ya kirayi Taliban da ta rungumi zaman lafiya.
Kamfanin Dillancin Labarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ambato Hikmater yana mika ta'aziyyar kisan da aka yi wa shugaban Taliban, Akhtar Muhammad Mansur, sannan kuma ya yi kira ga kungiyar da ta rungumi zaman lafiya.
A makon da ya shude ne dai kasar Amurka ta sanar da kashe, shugaban kungiyar ta Taliban Mullah Akhtar Mansur.
Hikmater dai da jam'iyyasa ta Hizbul-Islami da su ke dauke da makamai, sun yi nisa a tattaunawar sulhu da gwamnati, domin kawo karshen yaki.
Tags