MDD Ta Ayyana Kawo Karshen Yaduwar AIDS Kafin 2030
https://parstoday.ir/ha/news/world-i6484-mdd_ta_ayyana_kawo_karshen_yaduwar_aids_kafin_2030
MDD ta ayyana kawo karshen cutar AIDS/SIDA a siyasance, tare da yin alkawarin aiki tare da kasashe membobin ta don hana yaduwar cutar, da cimma burin da aka tsara kafin shekarar 2020, haka kuma, za su yi kokarin cimma burin kawo karshen yaduwar cutar kafin shekarar 2030.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 06:47 UTC
  • MDD Ta Ayyana Kawo Karshen Yaduwar AIDS Kafin 2030

MDD ta ayyana kawo karshen cutar AIDS/SIDA a siyasance, tare da yin alkawarin aiki tare da kasashe membobin ta don hana yaduwar cutar, da cimma burin da aka tsara kafin shekarar 2020, haka kuma, za su yi kokarin cimma burin kawo karshen yaduwar cutar kafin shekarar 2030.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, kasashen duniya sun samu gagarumar nasara a fannin yaki da yaduwar cutar AIDS, amma duk da haka ana bukatar karin lokaci don kawar da ita.

Kazalika Mr Ban Ya yi kira ga hukumomin lafiya na duniya da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kwamitin sulhu na MDD da su kara dora muhimmanci kan batun cutar AIDS, domin ci gaba da inganta hadin gwiwar kasashe daban daban wajen tinkarar cutar, sa'an nan a daina nuna bambanci ga mutanen dake fama da wannan cuta a lokacin da ake ba su jinya.