Magajin Garin Landan: Babu Wata Alaka Tsakanin Ta'addanci Da Musulunci
Magajin garin birnin Landan na kasar Birtaniya Sadiq Khan ya ce; babu wata alaka a tsakanin ta'addanci da kuma addinin muslunci.
Sadiq Khan ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Landan, inda ya ce ko alama 'yan ta'adda ba su wakiltar musulmi ko addinin mulsunci a cikin ayyukansu na ta'addanci, kuma abin da suke yi na kisan bil adama ba shi da wata alaka ko dangantaka da koyarwar musulunci.
Ya kara da cewa hadarin 'yan ta'adda masu da'awar jihadi bai takaita a kan wani ko wata al'umma ba, hadari wanda ya hada musulmi da wanda ba musulmi ba, domin kuwa akasrin mutanen da suka rasa rayukansu a duniya sakamakon hare-haren ta'addanci na masu da'awar jihadi musulmi ne.
Haka nan kuma ya yi kira da a dauki matakan da suka dace domin sanya ido kan masu yada akidar tsattsauran ra'ayi da kafirta al'umma a masallatai da gidajen talabijin da sunan wa'azi, domin kuwa a cewarsa akasarin masu irin wannan akidar a kasashen turai a cikin wadannan kasashen ne aka haife su, kuma a nan ake cusa musu irin wannan mummunar akida.